Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kashe wani jami’in ’yan sanda mai mukamin Assistant Superintendent of Police, Samaila Sule, tare da wasu mutum biyar a ƙauyen Farin Ruwa da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara.
Shaidun al’umma sun ce harin ya faru ne a ranar 5 ga Janairu, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye ƙauyen tare da rinjayar jami’an tsaro, inda daga bisani aka tsinci gawar ASP Samaila Sule a wurin harin.
Mutanen ƙauyen sun ƙara da cewa an kuma sace bindigar AK-47 ta jami’in da harsasai 30, yayin da aka gano gawar wasu mutum biyar, tare da sace wasu mazauna yankin wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

