Yan bindiga da ake zargin mabiyan fitaccen jagoran ta’addanci Bello Turji ne sun kai hari a Bargaje, ƙaramar hukumar Isa ta Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da mata tara. Shaidu sun ce maharan sun dira garin ne da daren Juma’a cikin tarin babura, suka yi harbi ba kakkautawa, suka kuma kona gidaje, abin da ya sa mazauna garin da dama gudu cikin daji domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ƙungiyar ‘yan sa-kai sun yi ƙoƙarin kare al’umma, amma sun kasa fafatawa da maharan saboda yawan su da irin makaman da suka zo da su. Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken jawabi ba game da adadin waɗanda suka rasa rayuwarsu, duk da cewa wani jami’in ƴan sanda ya tabbatar da faruwar lamarin.
A halin da ake ciki, hukumar ƙaramar hukumar Isa ta musanta zargin cewa shugaban ƙaramar hukumar, Sharehu Kamarawa, ya yi watsi da wani rahoton bayanan sirri da ya nuna yiwuwar harin kafin ya faru. A wata sanarwa da ta fitar, ta ce sun ɗauki matakin gaggawa ta hanyar tura ‘yan banga da sanar da hukumomin tsaro, sai dai maharan sun canza hanya suka afkawa Bargaje.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce suna ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kuma al’ummar da ke bada hadin kai wajen kare yankunan. Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji watsa jita-jita da kuma bayanai marasa tabbas da za su iya rage ƙarfin gwiwar masu kokarin kare rayuka da dukiyoyi. “Tsaro aiki ne na kowa; mu hadu mu kula da juna,” in ji shi.

