Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce idan ƴan Najeriya suka yi haƙuri, za a samu rayuwa mai inganci ta hanyar alkilta arziƙin ƙasa yadda ya kamata, abin da zai sa ƙasar ta yi fice a duniya a wannan sabuwar shekara ta 2026. Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin saƙon sabuwar shekara da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gini a kan sauye-sauyen da aka fara yi domin kyautata rayuwar al’umma.
Nasara a tattalin arziƙi duk da ƙalubale
Shugaban ya ce duk da irin ƙalubalen tattalin arziƙi da duniya ke fuskanta, gwamnatin sa ta samu gagarumar nasara a shekarar 2025, musamman a fannin tattalin arziƙi. Tinubu ya jaddada cewa sabuwar dokar haraji da aka fara aiki yanzu tana da nufin kawo sauyi wajen sauƙaƙa wa ƴan Najeriya biyan haraji fiye da kima, inda gwamnati za ta tattara kudaden shiga cikin adalci da tsari mai kyau.
Sauye-sauyen haraji don adalci da ƙarfi a kudaɗen shiga
Shugaban ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri yayin da ake aiwatar da sabon tsarin haraji, inda ya bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman manufofin tsarin shi ne kawo ƙarshen biyan haraji da yawa a matakai daban-daban na gwamnati. Tinubu ya yaba wa jihohin da suka amince da shiga tsarin harajin bai ɗaya, domin hakan zai sauƙaƙa wa jama’a biyan haraje-haraje a kan kayan abinci da sauran muhimman bukatu, da kuma dasa harsashin Najeriya mai adalci da ƙarfi a fannin kudaɗen shiga.

