Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu matasa uku da ake zargi da aikata fashi da makami da addabar mazauna Yola, babban birnin jihar. Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce an kama Auwal Inusa, Huzaifa Ahmed da Lukman Abdullahi, dukkansu ‘yan shekara 19, mazauna unguwar Nassarawo a karamar hukumar Yola North. An kama su ne da misalin karfe 3:00 na asuba, 5 ga Janairu, 2026, bayan sun shiga wani gida a Jimeta.
Rahoton ya kara da cewa mutanen gari ne suka cafke uku daga cikin su yayin da daya ya tsere, inda aka kwato wayoyi biyu, power bank, adda daya da wukake biyu. Kwamishinan ‘yan sanda, Dankombo Morris, ya yabawa hadin kan al’umma, yana mai cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.

