Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ceto mutane uku da aka sace a wani samame biyu da ta kai tsakanin jihohin Kano da Kaduna. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an gudanar da ayyukan ne tsakanin 7 zuwa 9 ga Oktoba 2025, bisa umarnin Kwamishina CP Ibrahim Bakori.
A samamen farko, jami’ai sun gano maboyar masu garkuwa a kauyen Saya-Saya, Ikara LGA ta Kaduna, inda aka ceto wani tsoho bayan wani matashi da ya tsere daga hannun masu garkuwar ya ba da bayanai akai. Masu laifin sun tsere suka bar babur da igiya.
A wani samame daban, an gano wani matashi da aka sace a Kano a gonar rake a Hunkuyi, Kaduna, inda aka ceto shi ba tare da rauni ba.
Kwamishina Bakori ya ce za su ci gaba da farautar masu laifin, tare da yabawa jami’an da suka gudanar da aikin.

