Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa gwamnati da manyan hafsoshin rundunonin tsaro za su kare duk wani soja da ke kan aikin sa bisa doka. Wannan na zuwa ne a lokacin da ake tunawa da sojoji da suka rasa rayukansu wajen kare kasa a bikin Armed Forces Remembrance Celebration and Remembrance Day na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.
Badaru ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake amsa tambayoyi daga ’yan jarida a taron manema labarai na ma’aikatar. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da ba jami’an tsaro kariya, musamman ma wadanda ke aiki cikin sahihanci da biyayya ga doka.
Maganar Ministan ta biyo bayan rikici da aka samu a ranar Talata tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyeson Wike, da wani Laftanar na Rundunar Sojan Ruwa, kan wata gona da ake zargin mallakar tsohon Babban Hafsan Sojan Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo.
Badaru ya kara da cewa: “Mun fara bincike a kan wannan lamari, kuma muna tabbatarwa cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka zai samu cikakken kariya. Ba za mu yarda a cutar da shi ba muddin yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata, kuma muna alfahari da yadda yake aiki.”

