Wani ƙwararren likitan kwakwalwa, Dr. Emmanuel Abayomi daga Asibitin Neuropsychiatric, Abeokuta a Jihar Ogun, ya bayyana cewa kusan mutane miliyan 60 a Najeriya na fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa a halin yanzu.
Ya bayyana haka ne a lokacin taron bita da ƙungiyar NAS Medical Mission ta shirya a Abeokuta, a cikin shirin bikin Ranar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta Duniya na bana.
Abayomi ya bayyana cewa kididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na nuna mutum ɗaya cikin takwas a duniya yana fama da wata matsalar kwakwalwa. Amma a Najeriya, adadin ya fi haka yawa — wanda ke nufin mutum ɗaya cikin biyar ko shida na fama da irin waɗannan matsaloli.
“Adadin masu fama da matsalolin kwakwalwa a Najeriya ya kai kusan miliyan 60, wanda ke nuna matsalar tana da tsanani,” in ji shi.
Ya lissafa damuwa (anxiety), baƙin ciki (depression), tasirin bala’i (post-traumatic stress), da kuma shan miyagun ƙwayoyi da giya a matsayin manyan abubuwan da ke haddasa matsalolin kwakwalwa. Haka kuma, zama cikin kaɗaici da dogon lokaci ana amfani da wayar salula na iya shafar lafiyar kwakwalwa.
Likitan ya shawarci jama’a da su kula da lafiyar kwakwalwarsu ta hanyar samun isasshen barci, cin abinci mai kyau, shan ruwa yadda ya kamata, motsa jiki, da kuma yin mu’amala da mutane. Ya kuma jaddada cewa “cututtukan kwakwalwa na iya warkewa idan aka nemi taimako da wuri.”

