Gwamnatin Tarayya tare da jihohi da sun ƙaddamar da gagarumin shirin rigakafin yara sama da miliyan 106 a fadin Najeriya, domin yaƙar cututtukan da ake iya daƙilesu ta hanyar alluran rigakafi. Shirin, wanda zai gudana daga Oktoba 2025 zuwa Fabrairu 2026, ya haɗa da rigakafin cututtuka kamar shan-inna (polio), mashako da rubella (measles–rubella), da kuma rigakafin HPV ga ‘yan mata ‘yan shekaru 9 zuwa 14, tare da rigakafin yau da kullum. Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta ƙaddamar da shirin a Abuja a ranar 6 ga Oktoba, inda ta bayyana shi a matsayin muhimmin mataki na kare rayuwar yara a Najeriya.
Shirin ya fara ne a jihohi 11 da Babban Birnin Tarayya, inda ake gudanar da wayar da kai ta hanyoyi daban-daban ciki har da amfani da motocin sanarwa, haɗin gwiwa da makarantu, iyaye, malamai, kungiyoyin addini da shugabannin gargajiya. Daraktan Rigakafi da Kula da Cututtuka na Hukumar NPHCDA, Dakta Garuba Rufai, ya bayyana cewa an haɗa wannan kamfen da shirye-shiryen lafiya kamar yaki da zazzabin cizon sauro da cututtukan da ake sakaci da su (NTDs).
A yayin da ake ci gaba da wannan shiri, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta jaddada muhimmancin rigakafi, tana mai cewa bai dace a ƙarni na 21 yara su ci gaba da kamuwa da cututtukan da za a iya kare su ba. Dr. Kumshida Balami, mai kula da shirin WHO a FCT, ta bayyana cewa rigakafi abin dogaro ne kuma mai aminci, tana kira ga iyaye da masu kula da yara su tabbatar da cewa an yi wa dukkan yara rigakafi don kare su daga makanta, raunin ji, lahani ga kwakwalwa da mace-mace sakamakon mashako ko rubella.
Daraktan Hukumar NPHCDA, Dakta Muyi Aina, tare da Sakataran Lafiya na FCTA, Dakta Adedolapo Fasawe, sun jagoranci ƙungiyar sa ido domin tantance yadda aikin ke gudana a cibiyoyin lafiya a Abuja da Kogi. Sun yaba da jajircewar ma’aikatan lafiya tare da tabbatar musu cewa gwamnati na aiki don magance ƙalubalen da suke fuskanta a karkashin shirin gyaran lafiyar “Renewed Hope”. Haka kuma sun yi kira ga iyaye da al’umma da su fita kwansu da kwarkwata su kai ‘ya’yansu wurin yin rigakafi, domin kare su daga cututtuka da za su iya hana su kai matsayin da Allah Ya tsara musu.

