Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta yi gargaɗi ga Gwamnatin Tarayya cewa za ta kira yajin aiki na ƙasa baki ɗaya idan bata kammala tattaunawa da ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu ba cikin mako hudu. Wannan na zuwa ne bayan ganawar gaggawa da NLC ta gudanar da shugabannin ƙungiyoyin ilimi ciki har da ASUU, SSANU, COEASU da ASUP, domin neman mafita ta dindindin ga matsalolin da ke addabar jami’o’i da sauran manyan makarantu a ƙasar.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa ƙungiyar ba za ta ci gaba da jure sakaci da jinkirin gwamnati ba, yana mai cewa idan har gwamnati ta kasa warware rikicin cikin wa’adin da aka bayar, to “za mu dakatar da aiki a fadin ƙasa.” Ya soki tsarin “ba aiki, ba albashi” da gwamnati ke amfani da shi, yana mai cewa daga yanzu za su ɗauki sabuwar matsaya ta “ba biyan albashi, ba aiki,” domin mafi yawan yajin-aikin ma’aikata a Najeriya na faruwa ne saboda rashin cika alkawarin gwamnati.
A bangaren su kuwa, ƙungiyar ASUU ta ce ba za ta sake shiga tattaunawa da wakilan gwamnati marasa ikon yanke hukunci ba. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta daina raina ƙungiyoyin ilimi, ta kuma ɗauki bangaren ilimi da muhimmanci. Ya kuma yi nuni da cewa duk da ikirarin Ministan Ilimi, Tunji Alausa, cewa an saki ₦50bn don alawus da kuma ware ₦150bn a kasafin 2025, malaman jami’a suna buƙatar cikakken aiwatar da yarjejeniyar 2009 da biyan albashin watanni uku da rabi da aka hana su.
A yanzu dai, yajin aikin ASUU ya shiga rana ta takwas a yau Talata, 21 ga Oktoba, 2025, kuma ƙungiyoyin ƙwadago na nuna cewa wannan rikici na iya girma zuwa yajin aiki na ƙasa idan gwamnati ta ci gaba da nuna halin ko-in-kula.

