Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kuɗaɗen da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta ƙwato daga hannun masu laifi, waɗanda suka haura naira biliyan 500, an sake juyar da su domin tallafawa shirye-shiryen jin ƙai na gwamnati. Tinubu ya ce cikin shekara biyu da suka gabata, EFCC ta samu gagarumar nasara wajen kwato kadarori da kuɗaɗe tare da gurfanar da sama da mutane 7,000 da ake zargi da laifin rashawa da almundahana.
Shugaban ƙasar, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta a taron bita na masu shari’a a Abuja, ya ce kudaden da aka dawo da su daga hannun barayin gwamnati an yi amfani da su wajen shirye-shiryen kamar lamunin ɗalibai da kuma tsarin bayar da bashi ga masu amfani da kayayyaki (consumer credit), domin rage wahalar tattalin arziki ga talakawa. Ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ba da goyon baya ga hukumomin yaƙi da rashawa domin tabbatar da gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin shari’a.
A nasa jawabin, Shugaban EFCC Ola Olukoyede ya koka kan jinkirin da ake samu a shari’o’in da suka shafi manyan mutane, yana mai cewa wasu shari’o’i na ɗaukar shekaru 15 zuwa 20 saboda dabarun da masu laifi ke amfani da su wajen jinkirta hukunci, ciki har da fakewa da rashin lafiya da ƙorafe-ƙorafen kotu. Ya ce irin wannan dabarun na hana gwamnati samun damar amfani da kadarorin da aka kwato cikin lokaci.
Olukoyede ya kuma yi kira ga alkalai da lauyoyi su guji kare masu laifi ko bayar da umarni marasa hurumi da ke hana EFCC gudanar da aikinta. Ya ce dole ne a tsabtace tsarin shari’a domin tabbatar da cewa duk kuɗin da aka kwato daga hannun masu satar dukiyar jama’a suna komawa cikin tattalin arzikin ƙasa ta hanyar ayyukan da ke amfani wa al’umma.

