Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya sanar da shirinsa na gudanar da aikin gyaran cibiyoyin sadarwa a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025, wanda zai shafi wasu yankuna a jihohin Kano, Borno da Adamawa. A cewar kamfanin, aikin zai ɗauki sa’o’i biyu (6:00 na safe zuwa 8:00 na safe), inda zai janyo ɗan tsaiko ga masu amfani da layin MTN a yankunan da abin ya shafa.
Kamfanin ya bayyana cewa gyaran ya shafi shafuka 101 a cikin ƙananan hukumomi 15, ciki har da Nasarawa a Kano, Girei, Mubi, Hong, Gombi, Fufore, Michika, Madagali, Chibok da Yola North a Adamawa, da kuma Askira/Uba da Shani a Borno. Wannan aikin, in ji MTN, na daga cikin shirin da ake yi na inganta hanyar sadarwar fibre domin tabbatar da ingantacciyar sadarwa a arewacin ƙasar.
A cewar sanarwar, aikin zai haɗa da mayar da sabon igiyar fibre tsakanin AFCOT da Bawo Village, inda za a sauya tsofaffin igiyoyi da suka lalace domin rage matsalolin da ke haifar da raunin sadarwa da yankewar layi. Wannan mataki, in ji MTN, na zuwa ne bayan aikin farfaɗo da hanyar sadarwa da aka gudanar a watan Agusta 2025 a yankin.
Kamfanin ya roƙi haƙurin abokan hulɗarsa bisa jinkirin da za su iya fuskanta yayin aikin, yana mai cewa wannan gyaran zai tabbatar da dogon lokaci na kwanciyar hankali da ƙarfi ga hanyar sadarwa. “MTN na ba da haƙuri kan duk wata damuwa da hakan zai iya haifarwa, kuma muna godiya da fahimtar abokanmu,” in ji sanarwar.

