Sojojin Najeriya sun kashe akalla ‘yan bindiga 80 da suka yi yunkurin shigowa Jihar Kebbi daga iyakar Zamfara, a wani gagarumin samame da aka bayyana a matsayin babbar nasara wajen yaki da ta’addanci a yankin. Kakakin Gwamnan Jihar Kebbi kan Harkokin Yada Labarai, Abdullahi Idris Zuru, ya ce wannan nasara ta biyo bayan umarnin Gwamna Nasir Idris na tura karin dakarun soji da kayan aiki domin tsaurara tsaro a kan iyakokin jihar da Zamfara, Sokoto da Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa rundunar soji ta kai farmaki a yankin Makurdi da ke Karamar Hukumar Ngaski, inda aka yi artabu mai zafi tsakanin sojoji da ‘yan bindigar a daren Juma’a da Asabar. A cewar jami’an tsaro, an halaka ‘yan bindiga 80 yayin da da dama suka tsere da raunukan harbi, tare da kwato babura da kuma ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Gwamnatin jihar ta ce wannan nasara ta zama sakamakon hadin gwiwa da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankuna masu fama da hare-hare. Haka kuma, Gwamna Idris ya riga ya bai wa dakarun tsaro motocin Hilux 100 da babura 5,000 domin inganta motsi da saurin daukar mataki kan barazanar tsaro.
Mai martaba Sarkin Yauri, Alhaji Zayyanu Muhammad, ya yaba da jarumtakar dakarun soji tare da jinjinawa kokarin Gwamna Idris wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Rahotanni sun ce wannan samame ya tilasta wa wasu kungiyoyin ‘yan bindiga komawa cikin dazukan da ke makwabtaka, abin da ke nuna cewa Kebbi ta fara zama yankin da ke da tsaro ga al’umma.

