Shugaban Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS), Dakta Zacch Adedeji, ya bayyana cewa hukumar ta samu gagarumar nasara wajen tara haraji inda ta tattara Naira tiriliyan 22.59 tsakanin watan Janairu zuwa Satumba, shekarar 2025. Haka kuma, daga watan Oktoba 2023 zuwa Satumba 2025, hukumar ta tara jimillar Naira tiriliyan 47.39 — wanda ya zarce kashi 115 cikin 100 na burin da aka sa mata. Adedeji ya ce wannan ci gaban ya nuna yadda tsarin harajin ƙasar ke sauyawa zuwa ga ingantacciyar hanya ta zamani da ke tallafawa tattalin arzikin ƙasa.
Ya bayyana cewa kudaden da aka samu daga bangaren da ba na mai ba (non-oil revenue) sun kai kashi 76 cikin 100 na dukkanin kudaden da aka tara, wanda ya nuna an samu nasarar rage dogaro da man fetur. Adedeji ya ce kudaden harajin mai sun kai Naira tiriliyan 5.29, yayin da bangaren da ba na mai ba ya kai Naira tiriliyan 17.3, wanda ya ninka burin da aka sa. Haka kuma, hukumar ta kafa tarihin cimma kashi 137 cikin 100 a harajin VAT da ake karɓa a cikin gida, da kashi 131 cikin 100 na VAT da ake karɓa daga kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Adedeji ya ce hukumar ta FIRS za ta canza suna zuwa Nigeria Revenue Service (NRS) daga ranar 1 ga Janairu, 2026 — domin faɗaɗa aikinta zuwa tara kuɗaɗen da ba haraji ba daga hukumar NUPRC. Ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙaddamar da muhimman shirye-shiryen zamani kamar tsarin National Single Window Project, da ke haɗa hukumomi da tashoshin jiragen ruwa don sauƙaƙa harkokin kasuwanci, da kuma tsarin e-invoicing, wanda ke ƙara inganci da gaskiya a fannin biyan haraji.
A ƙarshe, shugaban hukumar ya ce FIRS na ci gaba da zama cibiyar zamani mai dogaro da fasaha, da ke tafiyar da tsarin haraji bisa gaskiya, sauƙi da haɗin gwiwa da ‘yan kasuwa. Ya ce hukumar na shirin gudanar da “tax clinic” a faɗin ƙasar don ƙarfafa ilimin biyan haraji, musamman ga ƙananan ‘yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, tare da tabbatar da cewa an samar da tsarin da zai inganta tattalin arzikin ƙasa cikin gaskiya da bayyananniyar hanya.

