Kungiyar hadin gwiwar kungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa (INGO Forum) ta yi gargaɗi cewa sama da yara 96,000 a jihohi shida na arewacin Najeriya — Adamawa, Borno, Katsina, Sokoto, Yobe da Zamfara — na cikin haɗarin mutuwa sakamakon matsanancin rashin abinci ami gina jiki. Shugaban Action Against Hunger, Thierno Diallo, ya bayyana cewa lamarin akwai tayar da hankali, inda ya ce kimanin mutane miliyan 31 ke fuskantar ƙarancin abinci a 2025, wanda hakan zai sa Najeriya ta zama ƙasar da ke da mafi girman matsalar abinci a duniya.
A cewar rahoton, hukumar UNICEF ta ruwaito cewa yara miliyan 11 ‘yan ƙasa da shekara biyar na fama da “ƙarancin abinci” inda suke cin abinci daga ƙananan rukunai, abin da ke ƙara musu yiwuwar fama da lalurar “wasting”. Haka kuma, Hukumar Abincin Duniya (WFP) ta yi hasashen cewa mutane miliyan 33 na iya fuskantar matsanancin yunwa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, musamman saboda rikice-rikicen tsaro, hauhawar farashi, da sauyin yanayi da ke lalata noma da rayuwa.
Diallo ya ce cikin watanni uku masu zuwa, yara 600,000 masu ƙasa da shekara biyar za su kasance cikin haɗarin matsanancin rashin abinci mai gina jiki, inda daga cikinsu yara 96,000 za su iya mutuwa idan ba su samu magani ba. Ya ƙara da cewa mata masu juna biyu da masu shayarwa sama da 800,000 ma suna cikin haɗari, yayin da kashi 32% na yara ƙasa da shekara biyar a Najeriya ke da matsalar “stunting” — rashin girma saboda rashin gina jiki.
Shugaban Save the Children International (Nigeria), Duncan Harvey, da wakilar Plan International, Helen Idiong, sun bukaci gwamnati da abokan hulɗa su ɗauki matakin gaggawa tare da ƙara saka hannun jari wajen yaki da yunwa. Sun bayyana cewa yunwa da rashin abinci mai gina jiki ba wai matsalar jin kai ba ce kawai, har ma da take hakkin ‘ya’yan Najeriya na rayuwa da ci gaba. Sun kuma bukaci ƙarfafa tallafin abinci, magungunan gina jiki, da tsare-tsaren kare talakawa daga matsalolin tattalin arziki a gaba.

