Majalisar Dattijai ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na ɗaukar lamuni na N1.15 triliyan daga kasuwar cikin gida domin cike gibin da ya rage a kasafin shekarar 2025. Wannan mataki ya biyo bayan rahoton Kwamitin Majalisar Dattijai na Bashin Cikin Gida da Na Waje da aka gabatar a zaman majalisar ranar Laraba 12 ga Nuwamba, 2025.
Rahoton ya nuna cewa Dokar Kasafin Shekarar 2025 ta tanadi kashe kuɗi na N59.99 triliyan, wanda ya haura N54.74 triliyan da fadar shugaban ƙasa ta fara da shi, inda hakan ya haifar da gibin kasafi na N14.10 triliyan. Daga cikin wannan adadi, an riga an amince da N12.95 triliyan a matsayin bashin, yayin da N1.15 triliyan ke nan bai samu ba.
Shugaba Tinubu ya nemi wannan sabon lamuni ranar 4 ga Nuwamba, inda ya bayyana cewa zai taimaka wajen tabbatar da aiwatar da dukkan shirye-shirye da ayyukan gwamnati da aka tsara a shekarar 2025.
Bugu da ƙari, wani kudurin da Sanata Abdul Ningi ya gabatar an amince da shi, inda aka umurci Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattijai da ya kara kulawa wajen tabbatar da cewa kudaden lamunin sun shiga inda ya dace kuma an yi amfani da su yadda aka nufa.

