Gwamnatin Tarayya ta sanar da janye manufar amfani da harsunan uwa a matsayin harshen koyarwa daga matakin firamare zuwa sakandare, inda ta ayyana Turanci a matsayin sabon harshen koyarwa a duk matakan ilimi a Najeriya. Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a taron “Language in Education International Conference 2025” da aka gudanar a Abuja, wanda Hukumar British Council ta shirya.
Alausa ya ce binciken da ma’aikatarsa ta gudanar ya nuna cewa koyar da yara da harsunan uwa ba ta inganta tsarin ilimi ba, hatta ta kawo koma baya wajen fahimta da sakamakon jarabawa. Ya bayyana cewa dalibai da dama suna kammala makaranta ba tare da kwarewa a karatu ko rubutu ba, saboda rashin daidaito wajen amfani da harsuna daban-daban a jihohi. “Mun ga yadda wannan manufa ta lalata tsarin ilimi – yara suna zuwa JSS ko SS ba tare da sun koyi komai ba, sannan su kasa cin jarabawa irin su WAEC da JAMB,” in ji shi.
Ministan ya ce bambancin harsuna a jihohin kasar, kamar yadda ake samu a Borno da Lagos, ya janyo wahalar aiwatar da manufar. Don haka gwamnati ta yanke shawarar komawa Turanci don tabbatar da daidaito da fahimta ga ɗalibai a fadin ƙasa. Ya kara da cewa sabuwar manufar za ta taimaka wajen inganta ilimi da daidaita koyarwa tsakanin yankuna daban-daban.
A nata jawabin, Daraktar British Council a Najeriya, Donna McGowan, ta ce taron ya bai wa masana, malamai da masu tsara manufofi damar tattauna hanyoyin inganta kwarewar Turanci da kuma tasirin harshe wajen inganta koyo a nahiyar Afirka da kasashen Asiya ta Kudu. Tsohuwar manufar harshe da aka kaddamar a 2022 ta yi niyyar kare harsunan gida da al’adu, amma ta gamu da cikas sakamakon karancin malamai, kayan koyarwa da yawaitar harsuna a kasar.

