Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Nnamdi Kanu Ya Nemi Kotu Ta Dakatar Da Yanke Masa Hukunci Zuwa Wani Lokaci Na Daban

      November 13, 2025

      NAFDAC Ta Lalata Magunguna Da Kayan Abinci Marasa Kyau Na Kimanin Naira Biliyan 20

      November 13, 2025

      Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Turanci a Matsayin Harshen Koyarwa a Makarantun Najeriya

      November 13, 2025

      Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Harajin Kashi 15% Kan Fetur Ɗin Da Aka Shigo Da Shi Ƙasar

      November 13, 2025

      Atiku Ya Ƙaryata Batun Baiwa Sojan Ruwa Sabuwar Mota

      November 13, 2025
    • Siyasa

      Engr. Sagir Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

      November 12, 2025

      Kotu Ta Sake Dakatar Da Babban Taron PDP

      November 11, 2025

      INEC Ta Ayyana Soludo a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

      November 9, 2025

      An Rantsar Da Shugaban Ƙasa Mafi Tsufa a Duniya

      November 7, 2025

      Gombe Na Amfana Da Cire Tallafin Man Fetur – Inuwa Yahya

      November 4, 2025
    • Addini

      Hukumar NAHCON Ta Sanar Da Rage Kudin Aikin Hajjin 2026

      November 10, 2025

      Ƙungiyoyin Fityanul Islam Da Samarin Tijjaniyya Sun Yi Ƙarar Gwamnatin Kano a Kotu

      November 5, 2025

      Saudiyya Ta Ragewa Najeriya Kujerun Hajjin 2026

      October 17, 2025

      Sarkin Musulmi Ya Buƙaci a Samar Da Dokokin Amfani Da Kafafen Sada Zumunta a Najeriya

      October 16, 2025

      Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Laifin Yin Aure Ba Tare Da Amincewar Iyayensu Ba

      October 13, 2025
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Sojojin Najeriya Sun Ƙwato lita 290,000 Na Man Fetur a Yankin Neja Delta

      October 21, 2025

      Ƴan Bindiga Sun Ƙwace Wayoyin Ƴan Sanda a Zamfara

      October 2, 2025

      Gwamnan Kano Ya Buƙaci Tinubu Ya Tsige Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar

      October 1, 2025

      Will Using a VPN on Phone Helps Protect You from Ransomware?

      January 14, 2021

      Popular New Xbox Game Pass Game Being Review Bombed With “0s”

      January 14, 2021
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » NAFDAC Ta Lalata Magunguna Da Kayan Abinci Marasa Kyau Na Kimanin Naira Biliyan 20
    Featured

    NAFDAC Ta Lalata Magunguna Da Kayan Abinci Marasa Kyau Na Kimanin Naira Biliyan 20

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanNovember 13, 2025No Comments2 Mins Read

    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC, ta fara kona kayayyaki marasa inganci da suka kai darajar sama da Naira biliyan 20 a birnin Ibadan, jihar Oyo. A cewar hukumar, an gudanar da aikin ne a wajen zubar da shara na Moniya domin hana irin waɗannan kayayyaki dawowa kasuwa su haifar da illa ga lafiyar jama’a.

    Daraktar Janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, wacce mataimakiyarta, Mrs. Florence Uba ta wakilta, ta bayyana cewa kayayyakin da aka lalata sun haɗa da magunguna na jabu, kayan abinci marasa kyau, sinadarai masu haɗari, da kayan kwalliya da suka lalace. Ta ce an kwace kayayyakin daga masana’antu, ‘yan kasuwa, da kuma masu shigo da kaya daga waje, yayin da wasu kamfanoni masu bin doka suka mika nasu da suka lalace da kansu.

    Farfesa Adeyeye ta gode wa Hukumar Kwastam wadda ta mika wa NAFDAC akalla kwantena 25 na kayayyakin da ta kama domin a lalata su. Haka kuma ta yabawa jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda, sojoji, DSS, da sauran hukumomi bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar wajen kare lafiyar al’umma.

    NAFDAC ta yi kira ga shugabannin al’umma, likitoci, malaman addini da ‘yan jarida da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan haɗarin siyan magunguna daga masu sayarwa ba bisa doka ba. Haka kuma ta bukaci jama’a su rika ba da rahoton duk wata shakka da suka samu kan magunguna ko kayan abinci domin a kare rayukan ‘yan ƙasa.

    (NAFDAC)
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleGwamnatin Tarayya Ta Ayyana Turanci a Matsayin Harshen Koyarwa a Makarantun Najeriya
    Next Article Nnamdi Kanu Ya Nemi Kotu Ta Dakatar Da Yanke Masa Hukunci Zuwa Wani Lokaci Na Daban
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Nnamdi Kanu Ya Nemi Kotu Ta Dakatar Da Yanke Masa Hukunci Zuwa Wani Lokaci Na Daban

    November 13, 2025
    Featured

    Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Turanci a Matsayin Harshen Koyarwa a Makarantun Najeriya

    November 13, 2025
    Featured

    Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Harajin Kashi 15% Kan Fetur Ɗin Da Aka Shigo Da Shi Ƙasar

    November 13, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202537 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202536 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202527 Views

    Matuƙar Ba’a Yi Yadda Aka Yi a Afghanistan Ba Baza’a Kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya Ba – Amurka

    November 6, 202522 Views

    Zama a Banɗaki Fiye Da Kima Kan Haifar Da Matsala Ga Lafiyar Ɗan Adam – Likita

    October 28, 202520 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2025 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.