Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana ƙoƙari matuƙa domin kawo ƙarshen yawan lalacewar layin dogo da ake fuskanta a ƙasar nan. Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Muhammadu Mamman, ya wakilta a taron NISO na farko da aka gudanar a Uyo, ya ce tun zuwan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu an fara aiwatar da sabbin matakai domin inganta layin dogo da rage yawan katsewar wuta.
Adelabu ya bayyana cewa kafa hukumar Nigerian Independent System Operator (NISO) wani sabon salo ne da gwamnati ta ɗauka domin tabbatar da daidaito da ingantacciyar tafiyar da tsarin wutar lantarki. Ya ce wannan sabon tsari zai taimaka wajen rage dogaro da tsofaffin hanyoyin da suka janyo matsaloli da dama, ciki har da tsohuwar hanyar sadarwa, ƙarancin kuɗaɗen gyara da kuma matsalar lalata kayan lantarki ta hanyar vandalisam. Ya kuma yi nuni da cewa shirin taron NISO zai buɗe dama ga tattaunawa da gano sabbin dabaru na tabbatar da wutar lantarki mai dorewa.
A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar NISO, Dr. Adesegun Akin-Olugbade, ya yaba wa jajircewar ma’aikatan NISO, yana mai cewa jajircewarsu ta kai ga nasarar daidaita grid ɗin Najeriya da na West African Power Pool (WAPP) na tsawon sa’o’i hudu ba tare da tangarda ba. Wannan, a cewarsa, ya nuna amincin tsarin da kuma ƙwarewar ma’aikatan da ke kula da harkokin wutar lantarki a matakin ƙasa da yankin Afirka ta yamma.

