Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Sokoto ta kama mutane uku da ake zargi da fashi da makami, bayan satar babur din adaidaita sahu a hannun Usman Babangida. Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 13 ga Oktoba, 2025, a yankin Diplomat, lokacin da wadanda ake zargin suka tare Babangida don ya kai su Dambowa, amma suna cikin tafiya ne suka daureshi kuma suka gudu da babur din.
‘Yan sanda sun ce bayan samun rahoton, jami’an sashen bincike na Anti-Fraud sun gudanar da bincike har aka gano wadanda ake zargin a karamar hukumar Argungu ta Jihar Kebbi, inda suke shirin sayar da baburin da suka sata. An kuma kwato abin da aka sace, sannan an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Sokoto ya yabawa jami’an bisa saurin gudanar da aikin, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da yaki da laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Haka nan ya bukaci jama’a su ci gaba da bayar da sahihan bayanai a kan laifuka domin saukaka wa ‘yan sanda gudanar da ayyukansu.

