A ranar Laraba, 20 ga Nuwamba, 2025, rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta ce ta dakile yunƙurin sace wani mazaunin ƙauyen Guto da ke kan iyaka a ƙaramar hukumar Bwari. Kusan mutane 30 ne suka kai hari a ƙauyen, inda suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin gidan wanda aka yi niyyar daukewa.
A cewar kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, jami’an ‘yan sanda na Bwari Division Surveillance Team da IGP Special Intervention Squad sun kai hari cikin sauri, inda aka yi musayar wuta da masu laifi. Wannan ya yi sanadiyyar kashe mutum biyu daga ɓangaren ‘yan fashin, yayin da sauran suka tsere cikin daji.
Rahoton Bechi Hausa News ya gano cewa ɗaya daga cikin ‘yan sandan da suka yi musayar wutar ya samu raunuka masu tsanani kuma an tabbatar da mutuwarsa a asibitin Bwari General Hospital. Hukumar ‘yan sanda ta yaba jajircewar jami’in da ya mutu yayin aikin kuma ta yi ta’aziyya ga iyalansa.
Babban kwamishinan ‘yan sanda na FCT, CP Miller Dantawaye, ya yi kira ga mazauna ƙauyen Guto da sauran al’ummomi su ci gaba da lura da yanayi da bayar da rahoton duk wani motsi da ya saba wa doka ta hanyoyin gaggawa: 08032003913 ko 08068587311.

