A ranar Juma’a, 21 ga Nuwamba 2025, Hukumar Kula da Ma’aikatan Jihar Bauchi ta dakatar da manyan jami’ai hudu na Bill and Melinda Gates College of Health Sciences Technology da ke Ningi, bisa zargin aikata manyan laifuka a wurin aiki. Sanarwar da PRO na hukumar, Saleh Umar, ya fitar ta ce an dauki matakin ne domin tsabtace harkokin gwamnati da tabbatar da bin dokokin ma’aikata.
Hukumar ta bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun hada da Darakta Garba Hussaini, Haruna Umar, Umar Yusuf da kuma Mohammed Usman. An sanya su kan kaso 50 cikin 100 na albashi tun daga 28 ga Oktoba 2025, yayin da ake ci gaba da bincike kan zargin karya dokokin aikin gwamnati, musamman wadanda suka shafi sabawa ƙa’idojin gudanar da aiki da kuma rashin mutunta ka’idojin hukunci.
A cewar kakakin hukumar, yayin da ake dakatar da wadannan jami’ai, an kuma daukaka darajar ma’aikata 21 zuwa matakai daban-daban, wani mataki da ya nuna sahihancin kokarin gwamnati wajen karfafa wa nagari gwiwa. Shi ma shugaban hukumar, Dr Ibrahim Muhammad, ya jaddada kudirin hukumar na kare gaskiya, daidaito da kuma yin aiki bisa doka ga dukkan ma’aikata.
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa tana da kudirin hukunta duk ma’aikacin da ya saba dokoki, tare da tunatar da jama’a cewa a baya ta kora manyan jami’ai biyu saboda jabun takardu. Domin haka, ta bukaci ma’aikata su san dokokin da ke jagorantar aikinsu don kauce wa hukunci mai tsanani.

