Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta soki matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye ’yan sanda daga hidimar VIP, tana mai cewa wannan salon siyasa ne kawai da ba zai kawo sauyi wajen magance rikicin tsaro da ke addabar Najeriya ba. Jam’iyyar ta ce matakin ya nuna gazawar gwamnati wajen fahimtar girman matsalar tsaro da kuma irin tsarin da ake bukata don shawo kanta.
A cikin wata sanarwa da kakakinta, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta jaddada cewa wannan ba sabon mataki ba ne, domin a bana an bayar da irin wannan umarni sau biyu daga IGP amma babu wani abu da ya canza. Ta kara da cewa, ko da an sake tura ’yan sanda 100,000 daga hidimar VIP zuwa aikin tsaro, hakan ba zai magance matsalar ba, saboda ’yan sandan ba su da horo, kayan aiki da kuma tsarin da ya dace da yaki da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.
ADC ta yi nuni da cewa maye gurbin ’yan sanda da jami’an Civil Defence a matsayin masu kula da VIP ba shi da ma’ana, domin NSCDC na da wata dabamiyar manufa ta kariyar al’umma da rage hadurran bala’i. Jam’iyyar ta ce Najeriya na bukatar cikakkiyar dabarar tsaro ta kasa wacce za ta hada dukkan hukumomin tsaro cikin tsari guda, tare da modernisation, leken asiri da hadin kai.
A karshe, jam’iyyar ta kalubalanci gwamnatin Tarayya ta bayyana hujjojin da suka tabbatar da cewa an janye jami’an ’yan sanda 100,000 daga hidimar VIP kamar yadda ta sanar. Ta ce abin da ake bukata shi ne sake fasalin hukumomin tsaro gaba daya, ba sauya wurin aiki ko kirkirar manyan kanun labarai domin nuna aiki ba.

