Babban Limamin DaaruNaim Central Mosque, Lagos, Sheikh Imran AbdulMajeed Eleha, ya ce ba Musulmi na gaskiya ne ke aikata kashe-kashe ko kai farmaki kan Kiristoci ba, yana mai cewa addinin Musulunci ya haramta cutar da kowa. Ya bayyana hakan ne a hira da Punch a ranar 29 ga Nuwamba, 2025, inda ya ce Qur’ani ya umurci musulmi da adalci da kyautatawa ga duk wanda bai yi musu fada ba.
Sheikh Eleha ya ce wadanda ke kiran kansu da sunan musulmi suna kashe mutane suna daga cikin Khawarij, wadanda Annabi ya yi hasashen bullarsu. Ya ce Shari’a ba ta bai wa mutum damar kashe wani ba, kuma duk wanda ke amfani da “Allahu Akbar” wajen aika mummunan laifi ba Musulmi ba ne. Bechi Hausa ta lura cewa malamin ya jaddada cewa Boko Haram da ISWAP ba su wakiltar Musulunci, domin akidarsu bata ce, kuma matsalolin yanbindiga siyasa ce, ba addini ba.
Malamin ya ce yawancin wadanda bandits ke kashewa Musulmai ne, don haka kuskure ne a rika danganta rikicin Arewa ga addini. Ya kuma yi zargin cewa akwai manyan mutane da ke daukar nauyin miyagun, saboda kudaden da ake karba a cikin daji ba su da amfani ga ’yan bindiga muddin ba a garuruwa ake sarrafa su. Ya ce gwamnati na iya shawo kan matsalar idan ta kama masu daukar nauyin ta’addanci.
A karshe, Sheikh Eleha ya ce dole gwamnati ta magance tushen matsalar, ta hada malamai Musulmi da Kiristoci wajen wa’azi domin rage tsaurin ra’ayi. Ya bayar da misalin yadda Saudi Arabia ta yi amfani da tsarin yafiya wajen murkushe Al-Qaeda. Ya kara da cewa dangantaka tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya lafiya lau take, matsalolin kuwa siyasa ne, ba rikicin addini ba.

