Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da kashe wani ɗan fashi da makami tare da kama wasu uku bayan ta tarwatsa wasu hare-haren fashi biyu da suka auku safiyar Alhamis, 27 ga Nuwamba 2025. Lamarin ya faru ne a Hadejia da kuma Sule-Tankarkar, inda jami’ai suka yi artabu da ‘yan ta’adda da suka kai farmaki wurare daban-daban.
Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya ce a Hadejia, ‘yan fashi kimanin takwas sun kai hari kamfanin Fruska Table Water da misalin 3:35 na safe, inda suka bude wuta ga jami’an da suka isa cikin gaggawa. Bechi Hausa ta tattaro cewa ɗaya daga cikin barayin ya mutu bayan harbin da ya sha, yayin da sauran suka tsere, inda aka kwato baka, kibau, gatari da sauran muggan makamai.
A wani samame daban, jami’an Sule-Tankarkar sun cafke wani ɗan fashi bayan sun yi ram da uku da suka saci babura biyu a Togai. Dayansu ya tsere zuwa cibiyar kiwon lafiya, inda jama’a suka yi masa dukan barna kafin jami’an su karɓe shi, tare da kwato bindiga da baburan da aka saci.
Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin cafke sauran wadanda suka tsere, yayin da wanda aka kama zai fuskanci shari’a nan ba da jimawa ba. SP Adam ya bukaci jama’ar Jigawa su ci gaba da bada bayanai cikin lokaci don taimakawa kokarin tabbatar da tsaro a jihar.

