Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana gudanarwa. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Muhammad Sulaiman, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X, bayan zaman majalisar zartarwa.
Sanarwar ta bayyana cewa an dakatar da yajin ne na tsawon mako huɗu, bayan cimma wasu muhimman yarjejeniyoyi da gwamnatin tarayya game da buƙatun ƙungiyar guda 19. Daga cikin manyan matsalolin da aka fara warwarewa har da batun biyan kuɗin ƙarin matsayi, bashin albashi da ake binsu, da kuma alawus na musamman.
Bechi Hausa ta gano cewa ƙungiyar na sa ran gwamnati za ta kammala biyan wadannan muhimman hakkoki cikin makonni biyu masu zuwa, domin magance matsalolin da suka haddasa yajin. NARD ta ce dakatarwar ba ƙarshen yajin ba ne, sai dai dama ga gwamnati ta cika alkawuranta.
Yajin aikin da likitocin suka yi ya jefa wasu asibitoci cikin tsaiko mai tsanani, inda marasa lafiya suka dinga korafin rashin samun likitoci, lamarin da ya yi barazana ga lafiyar al’umma a sassa daban-daban na ƙasar.

