Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da aniyar ta na kawo karshen cutar AIDS a 2030, inda ƙaramin Ministan Lafiya Dr Iziaq Salako ya ce an saka fiye da N300bn domin ƙarfafa gwaji da magani. Ya bayyana haka yayin bikin Ranar AIDS ta Duniya mai taken “Overcoming Disruptions; Sustaining Nigeria’s HIV Response.”
Ya ce sama da mutane miliyan 1.6 na shan magani daga cikin kimanin miliyan 1.9 masu cutar a ƙasar, tare da fadada samar da magunguna da kayan gwaji a cikin gida. Haka kuma gwamnatin Shugaba Tinubu ta ci gaba da aiwatar da shirin Free to Shine domin hana yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri da kuma inganta jiyya.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yaba da ci gaban da aka samu, tana jaddada bukatar ƙarin jajircewa da kawar da wariya ga masu cutar.
Hukumar NACA ta ce an rage yawan masu cutar zuwa kaso 1.4%, duk da matsin tattalin arziki da raguwar tallafin waje. Gwamnatin tarayya ta kuma ware dala miliyan 200 domin tallafawa shirye-shiryen HIV, tana kira ga jihohi su karɓi ragamar cigaban yaki da AIDS a ƙasar.

