Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen Seme ta bayyana cewa ta tara sama da Naira biliyan 2.5 cikin watan Oktoba na bana. Wannan na zuwa ne a wani gajeren biki da aka shirya domin karrama jami’ai biyu da suka yi fice a aikin su.
A jawabin sa, Kwamptrolan Kwastam na Seme, Wale Adenuga, ya ce ƙwazon ma’aikatan ne ya haifar da wannan karuwar kudaden shiga, inda har kuma aka kama kayayyakin da kudin harajin su ya kai N1.99bn. Cikin abin da aka kama har da buhuna 10,000 na fulawa daga Masar wadda ta lalace, da darajar N1.21bn.
A cikin jerin kayan da aka kwace akwai tabar wiwi (1,104 parcels), tramadol, buhunan shinkafa 2,043, kaya na OKirika 150 bales, hodar tari mai codeine guda 169, da motoci biyu riga guda biyar. A cewar Adenuga, ƙwazon jami’an ya taka rawar gani, lamarin da ya kara wa hukumar samun nasara — kamar yadda Bechi Hausa ta ruwaito.
Kwamptrolan ya ƙara da cewa idan har ci gaban da ake gani ya ci gaba, akwai yiwuwar samun kudaden shiga fiye da Naira biliyan 3 kafin ƙarshen zangon hudu na shekarar 2025.

