Jami’an ‘yan sandan jihar Borno sun tabbatar da cewa wani abin fashewa ya kashe matasa hudu a Banki, karamar hukumar Bama. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:40 na ranar Juma’a a bayan tashar motar Banki da ke unguwar Wajari, inda matasan suka ci karo da nakiyar inda su ka dauko ta. Wadanda suka rasu sun hada da Awana Mustapha mai shekaru 15, Malum Modu 14, Lawan Ibrahim 12, da Modu Abacha 12.
Kakaki rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Nahum Daso, ya ce bincike ya nuna cewa yaran suna wasa da kayan ne a wani ɗaki na wucin-gadi kafin ya tashi ya hallaka su. Nahum ya kara da cewa wani yaro mai suna Mustapha Tijja, dan shekaru 12, ya tsira amma ya samu munanan raunuka, kuma yanzu haka yana jinya a asibitin NGO na FHI 360 da ke Banki. Bechi Hausa ta gano cewa kwararrun jami’ai a fannin tarwatsa bama-bamai tare da DPO na Banki sun isa wajen nan take domin kulle yankin da gudanar da bincike.
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa an dawo da zaman lafiya a yankin, kuma bincike ya ci gaba domin gano asalin kayan fashewar da yadda ya shiga hannun yaran. Wannan lamari ya sake jaddada matsalar baraguzan bamabamai da ke yawo a yankunan da rikici ya shafa, abin da ke haifar da barazana ga rayukan al’umma musamman kananan yara.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Naziru Abdulmajid, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa, tare da yin kira ga jama’a – musamman yara – da su guji taba ko wasa da kowanne abu da ba su sani ba. Ya bukaci al’umma da su rika kai rahoton dukkan kayayyakin da ake zargin na iya fashewa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin kare rayuka.

