A safiyar Lahadi, 7 ga Disamba 2025, gwamnatin Jamhuriyar Benin ta sanar da gaggarumin yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi amma ya ci tura. Ministan harkokin cikin gida, Alassane Seidou, ya bayyana hakan kai tsaye a gidan talabijin na ƙasar, yana mai cewa matakin ya nufi tayar da hankalin jama’a da rikitar da tsaron ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa rukunin sojoji ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanar Pascal Tigri ne suka bayyana hambarar da Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da tsarin mulki a talabijin. Har ila yau, sojojin sun yi ƙoƙarin bayyana cewa sun ɗauki ragamar mulki domin kare ƙasa daga abin da suka kira “matsaloli”.
Sai dai Minista Seidou ya ce rundunar sojan Benin ta nuna biyayya ga kundin tsarin mulki da rantsuwar da suka yi wa ƙasa, lamarin da ya ba su damar daƙile harin cikin gaggawa ba tare da samun wata barazana mai girma ga jama’a ba.
Gwamnatin Benin ta tabbatar cewa an shawo kan dukkan guguwar juyin mulkin, kuma an dawo da ƙasar karkashin cikakken ikon hukumomin da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya. An kuma ba da tabbacin cewa za a gurfanar da duk wanda ke da hannu a lamarin a gaban shari’a domin daƙile irin wadannan yunƙuri a nan gaba.

