Kamfanin sadarwa na Glo ya nemi afuwar kwastomominsa bayan rugujewar sabis na intanet da ta faru tun da safiyar Talata, ƙarfe 8:30 na safe, wadda ta shafi sassa daban-daban na ƙasar. A cikin sanarwar da ya fitar, Glo ya tabbatar da matsalar, yana mai cewa tawagarsa ta fasaha na aiki tukuru domin dawo da ingantaccen haɗin yanar gizo cikin gaggawa.
Kamfanin ya gode wa kwastomomi bisa haƙurin da suka nuna, yana jaddada muhimmancin samun tabbacin sabis mai ɗorewa. Glo ya kuma yi amfani da kafofin sada zumunta domin sanar da masu amfani da layukan Glo cewa ana ci gaba da warware cikas ɗin.
A ƙarshe, Glo ya gode wa kwastomomi saboda amincewa da kamfanin, tare da tabbatar musu da cewa sabis zai koma yadda ya kamata ba da jimawa ba.

