Kungiyar ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a dukkan kasashen Yammacin Afirka domin dakile barazanar juyin mulki da ke kara yawan faruwa a yankin, musamman bayan yunkurin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Benin kwanaki biyu da suka gabata. Matakin ya zo ne a yayin zaman Majalisar Tsaro ta ECOWAS karo na 55 da ake gudanarwa a Abuja.
Shugaban Hukumar Tsaro da Sasanci na ECOWAS, Omar Touray, ya bayyana cewa yawaitar katsalandan na sojoji a kasashen yankin, rashin bin tsarin sauyin mulki, da karuwar kungiyoyin ta’addanci na kara girgiza dimokuradiyya. Ya ce hakan ya sa wajibi ECOWAS ta kara zuba jari a tsaro da matakai na gaggawa domin kare yankin.
A cewar Touray, “zabe shi ne babban tushen rikice-rikice a al’ummomi,” inda ya kuma jaddada muhimmancin hadin guiwar yankunan da suka fice daga ECOWAS, musamman kasashen AES – Burkina Faso, Mali da Nijar.ya ce tattaunawa da tsauraran matakan tsaro su ne kadai hanyar hanawa juyin mulki sake tasowa.
Ya gargadi cewa halin da ake ciki bai taba faruwa ba a tarihin ECOWAS, yana mai bayyana lamarin a matsayin yanayin gaggawa. Ya bukaci a rika gudanar da zaman Majalisar Sulhu a kai a kai a shekara mai zuwa, tare da mayar da hankali kan batutuwan Guinea-Bissau, ta’addanci, iyakoki da matsin lamba daga kasashen duniya.

