Najeriya ta ƙulla sabon yarjejeniyar ƙawancen tsaro da Saudiyya domin ƙarfafa haɗin gwiwar soja da musayar bayanan tsaro. Masana harkokin diflomasiyya da tsaro sun bayyana matakin a matsayin wani muhimmin ɗan karon farko da zai iya faɗaɗa dangantakar duka ƙasashen biyu.
Sai dai masana sun yi kashedin cewa ko da yake yarjejeniyar na da amfani, ba za ta wadatar wajen magance matsalolin tsaron cikin gida da Najeriya ke fama da su ba, musamman matsalolin da suka shafi ‘yan bindiga, ta’addanci da rikice-rikicen yankuna. Sun ce dole ne gwamnatin Najeriya ta ci gaba da gyare-gyaren cikin gida da inganta ƙwarewar hukumomin tsaro.
Wata sanarwa daga Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta ƙasar ta tabbatar da cewa Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ne ya wakilci Najeriya yayin rattaba hannun, tare da takwaransa daga Saudiyya, Dr. Khaled H. Al-Biyari. Bechi ta tattaro cewa wannan dai na cikin ƙoƙarin gwamnatin Najeriya na neman ƙarin haɗin gwiwa da ƙasashen waje domin tallafa wa yunkurinta na yaki da rashin tsaro.
Masana sun ce duk da amfanin haɗin kan ƙasashen biyu, sai an ɗauki matakai na cikin gida kafin Najeriya ta sami dawwamammen sauyi a fannin tsaro. Sun jaddada cewa haɗin gwiwa da Saudiyya na iya zama kari, amma ba zai maye gurbin manyan shirye-shiryen ci gaba da ƙarfafa rundunonin tsaro na cikin gida ba.

