Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafa da Rarraba Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed, ya fito fili ya musanta wata doguwar sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka jingina masa a matsayin martani kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa. A cikin sanarwar musantawar da ya fitar, Ahmed ya ce bai taɓa rubuta ko amincewa da waccan sanarwa ba, yana mai jaddada cewa ba daga gare shi ta fito ba.
Ahmed ya ce yana sane da zarge-zargen da ake yi masa da iyalansa, da kuma ce-ce-ku-cen da suka biyo baya a bainar jama’a, amma ya zaɓi kauracewa muhawara a fili saboda yanayin aikinsa a matsayin jagoran hukuma mai muhimmanci. Ya bayyana cewa mutumin da ya shigar da ƙarar ya kai batun gaban hukuma ta doka, wato Hukumar ICPC, inda ya ce wannan ita ce hanya mafi dacewa da za a binciki gaskiyar lamarin tare da ba shi damar wanke sunansa.
Rigimar dai ta samo asali ne daga ƙarar da shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya shigar gaban ICPC, inda yake zargin shugaban NMDPRA da cin hanci, amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, da mallakar dukiya da ba a bayyana tushenta ba. ICPC ta tabbatar da karɓar ƙarar, lamarin da ya ƙara janyo hankalin ’yan majalisa, ƙungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki a harkar makamashi, yayin da ake kira da a bi doka da oda wajen binciken lamarin.

