Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya da ya fi kowane ɗan wasan ƙasar yawan cin ƙwallaye a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya, Ahmed Musa, ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙungiyar ƙasa wasa, lamarin da ya kawo ƙarshen doguwar hidimarsa ga ƙasar.
Musa, wanda ya shahara wajen taka rawar gani a manyan gasanni na duniya, ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan shafe shekara 15 yana wakiltar ƙungiyar Super Eagles, inda ya taimaka wajen ɗaukaka martabar ƙwallon ƙafar Najeriya a idon duniya.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, tsohon kyaftin ɗin Super Eagles ya bayyana cewa gudummawar da ya bayar wa ƙasar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa, yana mai jaddada cewa ya ɗauki matakin ne da cikakkiyar zuciya da godiya ga dukkan ‘yan Najeriya.

