An sako ragowar dalibai 130 da aka sace daga Makarantar St. Mary’s Catholic Primary da Secondary School da ke Papiri a Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Niger. Rahotanni sun nuna cewa an sake su ne a wani wuri da ke tsakanin ƙananan hukumomin Agwara da Borgu, bayan shafe kusan wata guda a hannun masu garkuwa da mutane.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Niger, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da sakin daliban, kodayake ya ce har yanzu ana tantance adadin su na ƙarshe. Haka nan, Bishop na Diocese na Kontagora kuma mai makarantar, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, ya ce Gwamna Mohammed Umaru Bago ne ya sanar da shi labarin, yana mai tabbatar da cewa dalibai da malamansu sun kubuta lafiya, kuma ana sa ran za su isa Minna domin tarbar hukuma a gidan gwamnati.
Tun da farko, ’yan bindiga sun kai hari makarantar a ranar 21 ga Nuwamba, 2025, inda suka sace mutane 315 da suka haɗa da dalibai 303 da malamai 12. Bayan wasu dalibai sun tsere, an rage adadin da ke tsare zuwa 265, kafin daga bisani a saki dalibai 100 a ranar 7 ga Disamba. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce sakin duka daliban ya biyo bayan aikin hadin gwiwar sojoji da bayanan sirri, kuma ana sa ran za su haɗu da iyayensu domin shagulgulan Kirsimeti.

