Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi kira da a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji da ake shirin fara aiki da ita daga ranar 1 ga Janairun 2026, sakamakon zargin cewa an sauya ko an yi cushe a cikin dokar ta hanyar da ta saɓa da abin da Majalisar Ƙasa ta amince da shi. Wannan zargi ya janyo muhawara mai zafi kan sahihancin dokar da tsarin samar da ita.
Batun ya fara bayyana ne makon da ya gabata, bayan wani ɗan Majalisar Wakilai daga Sokoto, Abdulsamad Dasuki, ya nuna cewa akwai bambance-bambance tsakanin dokar da majalisa ta amince da ita da wadda aka fitar a hukumance. A wata sanarwa da NBA ta fitar ranar Talata, ƙungiyar ta ce wannan al’amari na tayar da hankula game da gaskiya, sahihanci da amincin tsarin dokokin Najeriya.
Shugaban NBA, Afam Osigwe, ya jaddada cewa dole ne a dakatar da duk wani shiri na aiwatar da dokar har sai an gudanar da cikakken bincike a bayyane. Ya gargadi cewa ci gaba da aiwatar da dokar a halin da ake ciki na iya janyo matsalolin tattalin arziki, tayar da hankalin ’yan kasuwa da masu zuba jari, tare da haifar da rashin tabbas ga jama’a da hukumomin da dokar ta shafa.

