Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a mayar da Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, zuwa gidan gyaran hali na Kuje duk da ba shi beli na naira miliyan 500. Alkalin kotun, Justice Emeka Nwite, ya ce za a tsare shi har sai ya cika sharuɗɗan belin da kotu ta gindaya.
Alkalin ya bayyana cewa masu tsaya masa biyu dole su kasance masu fili a yankunan Maitama, Asokoro ko Gwarimpa a Abuja, tare da tantance takardun kadarorinsu. Ya kuma umarci a miƙa fasfofin ƙasashen waje da hotunan fasfo biyu ga rajistarar kotu, tare da hana shi fita daga ƙasar ba tare da izinin kotu ba.
Hukumar EFCC ta tuhumi Adamu da wani kamfani a kan zargin badaƙalar kuɗi sama da naira biliyan 4.6, inda ake zarginsa da taimakawa wajen karkatar da kuɗin da aka ware don sayen babura ga gwamnatin Bauchi a 2023. Kotu ta ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga Janairu, 2026, domin fara sauraron shari’a.

