Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen cewa za a samu hazo da guguwa da hasken rana daga ranar Asabar zuwa Litinin a fadin kasar. NiMet ta ce za a sami hazo a wasu sassan Borno, Jigawa, Katsina, Kano, Zamfara da Sokoto a ranar Asabar, yayin da sauran sassan Arewa za su kasance cikin rana mai ɗumi da haske.
A tsakiyar kasar, NiMet ta ce za a samu rana tare da ɗan gajimaren girgije, yayin da kudu za a samu hasken rana tare da ɗan girgije a lokutan safe. A wasu sassan kudu za a iya samun guguwa da ruwan sama a jihohin Abia, Imo, Anambra, Edo, Ekiti, Oyo, Ondo, Osun, Ogun, Lagos, Delta, Bayelsa, Cross River, Rivers da Akwa Ibom.
A ranar Lahadi, NiMet ta yi hasashen ƙura da hazo mai matsakaicin ƙarfi a Kano, Katsina, Bauchi, Gombe, Yobe, Jigawa da Borno tare da hangen nesa tsakanin kilomita 2 zuwa 5. Hukumar ta yi gargadi ga matafiya da masu fama da cututtukan numfashi da su yi taka-tsan-tsan, sannan ta shawarci kamfanonin jiragen sama su sami cikakken rahoton yanayi daga NiMet kafin gudanar da ayyukansu.

