Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta fara gudanar da matakan tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Oduh, bayan gabatar da sanarwar tuhuma kan zargin manyan laifuka a zaman majalisa da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta.
Shugaban masu rinjaye, Major Jack, ya karanta jerin tuhume-tuhume guda bakwai kan Fubara bisa sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulki, ciki har da rusa majalisar zartarwa, kashe kuɗaɗe ba tare da kasafin kuɗi ba, hana kuɗaɗen majalisa, da ƙin bin umarnin Kotun Koli kan ’yancin kuɗin majalisa.
Haka nan, an gabatar da tuhuma kan mataimakiyar gwamnan, Ngozi Oduh, bisa zargin kashe kuɗin jama’a ba bisa ka’ida ba da hana majalisa yin aikinta, inda ’yan majalisa 26 suka rattaba hannu, tare da bayyana cewa za a mika wa gwamnan sanarwar a cikin kwanaki bakwai.

