Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Yobe (YBSIEC) ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a faɗin kananan hukumomi 17 na jihar a ranar Asabar, 6 ga Yuni, 2026.
Sanarwar ta fito ne a Damaturu yayin taron masu ruwa da tsaki, inda wakilin hukumar, Mohammed Grema Nguru, ya bayyana cewa gwamnan jihar, Mai Mala Buni, ya amince da jadawalin zaɓen domin ƙarfafa dimokuraɗiyya a matakin ƙasa-ƙasa.
Hukumar ta ce za ta fitar da cikakkun ka’idojin zaɓe, tare da jaddada sharuddan takara da kuɗaɗen fom, inda ta tabbatar wa al’ummar Yobe cewa zaɓen zai kasance cikin gaskiya, adalci da zaman lafiya, tare da buƙatar haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki.

