Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani soja da jami’in Hukumar NSCDC a garin Udeku, yankin Turan da ke karamar hukumar Kwande a Jihar Benue. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, wanda ya tilasta wa mazauna yankin da dama guduwa daga gidajensu.
Wata majiya ta ce jami’an tsaron suna dawowa ne daga kasuwar Aga inda suka je siyan iskar gas, sai suka fada tarko bayan sun ci karo da shingen da ’yan bindigar suka kafa. An bayyana cewa an harbe su inda suka mutu nan take, kafin daga bisani matasan yankin su gano gawawwakin su.
Rundunar soji da NSCDC sun tabbatar da aukuwar lamarin, suna mai cewa jami’an suna aiki ne a karkashin Operation Whirl Stroke domin dakile hare-hare a yankin. Hukumar NSCDC ta ce duk da wannan asara, za ta ci gaba da jajircewa wajen yakar matsalar tsaro, yayin da shugabannin gargajiya da na kananan hukumomi ke nuna damuwa kan karuwar shigowar ’yan bindiga a Benue.

