Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya tabbatar da komawarsa jam’iyyar APC, bayan watanni biyu da korarsa daga jam’iyyar NNPP saboda zargin kin biyan kudin zamansa mamba da kuma aikata abin da aka kira da “siyasar cikin gida”. Jibrin, wanda ya kasance daga manyan magoya bayan Kwankwasiyya, ya dade ba tare da bayyana makomarsa ba, lamarin da ya sa ana alakanta shi da Shugaba Bola Tinubu saboda kusancin da ake ganin yana tsakanin su.
A wata sanarwa da ya wallafa ta shafukan sada zumunta, Jibrin ya ce shi da dubban magoya bayansa sun yanke shawarar ficewa daga NNPP da barin tafiyar Kwankwasiyya, tare da komawa APC domin goyon bayan Tinubu ya sake neman wa’adi a 2027. Ya ce al’umar yankinsa ne suka tsara wannan mataki domin ganin ana samun ci gaba da kwanciyar hankali a Kiru da Bebeji, da ma jihar Kano baki daya.
A yayin taron da aka gudanar a Kofa, Jibrin ya ce ya koyi darasi a baya, lokacin da ya sauya jam’iyya shi kadai, wanda ya haifar da cece-kuce kan ko yana da magoya baya ko babu. Saboda hakan, wannan karon ya ce ya zo da jama’arsa gaba daya domin tabbatar da cewa suna tare da shi, ba kawai ya sauya ne shi kadai ba.
Bugu da kari, fiye da malamai 2,000 daga yankin sun gudanar da addu’o’i na musamman domin samun nasara ga Shugaba Tinubu da kuma zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya. Wannan na zuwa yayin da siyasar Kano ke ci gaba da sauye-sauye, inda bangarori daban-daban ke sake daidaita matsayinsu gabannin babban zaben 2027.

