Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ƙasarsa na da isassun makaman yaƙi da za a iya amfani da su “har abada”, yana mai jaddada cewa a shirye take ta yi nasara a duk wani rikici. Ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin Truth Social.
Trump ya ce ana iya gudanar da yaƙe-yaƙe na dogon lokaci da irin makaman da Amurka ke da su kaɗai. Ya ƙara da cewa ƙasar na da tarin makamai marasa iyaka kuma a shirye take ta samu babbar nasara.
Shugaban ya kuma zargi tsohon shugaban ƙasa, Joe Biden, da bai wa Ukraine makamai masu ƙarfi ciki har da makaman linzami irin su ATACMS da ke iya kai hari har mil 190, kimanin kilomita 300.

