Ƙasar Amurka ta yi kakkausar suka kan harin da ya kashe mutane da dama a yankunan Woro da Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama a Jihar Kwara. Wannan na zuwa ne yayin da ake samun saɓanin adadin waɗanda suka mutu, inda ƴansanda suka ce mutum 75 ne suka rasu, yayin da wasu rahotanni ke nuna adadin ya fi haka.
A wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafin X ranar Juma’a, ya bayyana harin a matsayin abin firgici. Sanarwar ta ce fiye da mutane 160 ake fargabar sun mutu, tare da nuna alhini ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa.
Amurka ta kuma yaba da umarnin Shugaba Bola Tinubu na tura jami’an tsaro domin kare al’ummomin da abin ya shafa. Shugaban ya umarci tura bataliyar sojoji zuwa Kaiama tare da kafa sabon rundunar soji, yayin da sufeto-janar na ƴansanda ya tura jami’an dabaru da na leƙen asiri domin dawo da zaman lafiya.

