Shugaban Kamaru, Paul Biya mai shekara 92, ya sake karɓar rantsuwar zama shugaban ƙasa karo na takwas, duk da zanga-zangar da ta barke saboda zargin maguɗin zaɓe. A jawabinsa na farawa, Biya ya yi alƙawarin dawo da zaman lafiya, yana mai zargin wasu “’yan siyasa marasa hankali” da haddasa rikice-rikicen da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Sakamakon zaɓen ya nuna Biya ya samu kashi 54% na kuri’un da aka kaɗa, yayin da abokin hamayyarsa Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%. Sai dai Tchiroma ya yi zargin an yi maguɗi, inda ya ce shi ne ya yi nasara a zahiri. Wannan zargi ya tayar da tarzoma a sassa daban-daban na ƙasar, inda akalla mutane 14 suka rasa rayukansu, sama da mutane 1,200 kuma aka kama, a cewar Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta ƙasa.
A jawabinsa, Biya ya jinjina wa jami’an tsaro bisa yadda suka dakile zanga-zangar, amma bai tabo koken da ake yi na cin zarafin masu zanga-zanga ba. Ya kuma yi kira ga ƴan ƙasa da su manta da rikice-rikicen zaɓe su haɗa kai, tare da yin alƙawarin inganta rayuwar matasa da mata da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.
Tchiroma kuwa har yanzu bai janye matakinsa ba a matsayin shi ne ya ci, inda ya kira ga yajin aiki a wasu yankuna, musamman Garoua da Douala. Ya kuma bukaci ƙasashen ƙetare su sanya takunkumi ga jami’an gwamnati na Kamaru saboda abin da ya kira tsangwamar zabe da take hakkin ‘yan ƙasa. Duk da haka, Kotun Tsarin Mulki ta ƙasar ta ce babu hujjar da ta isa ta soke sakamakon zaɓen.

