Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Mutane 4 Sun Mutu a Turmutsutsun Karɓar Sadaka a Katsina

      March 2, 2026

      Ba Za Mu Bayar da Tabbacin Sahihin Zaɓe a 2027 Ba – Amupitan

      March 2, 2026

      Jirage Marasa Matuƙa Sun Kai Hari Matatar Man Saudiyya

      March 2, 2026

      Najeriya Ta Buƙaci a Kawo Karshen Rikicin Gabas ta Tsakiya

      March 2, 2026

      Iran Ta Naɗa Ayatollah Arafi A Matsayin Jagoran Addini Na Riƙo

      March 1, 2026
    • Siyasa

      Gwamnan Adamawa Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

      February 27, 2026

      NDLEA Ta Kama Wata Mata Mai Cikin Bogi Ɗauke da Hodar Iblis a Iyakar Seme

      February 22, 2026

      Jam’iyyun Adawa Sun Kaurace wa Zaɓen Kano, APC Ta Lashe Kujerun Majalisa a Rivers

      February 22, 2026

      Kotu Ta Umarci INEC Ta Yi Wa Jam’iyyar NDP Rajista

      February 19, 2026

      Gwamnan Zamfara Ya Zargi Gwamnatin Tarayya da Nuna Masa Wariya Saboda Bambancin Jam’iyya

      February 18, 2026
    • Addini

      Bauchi Ta neman ƙarin Kujerun Hajji Daga Saudiyya

      February 16, 2026

      Sarkin Musulmi Ya Umarci Ƴan Najeriya Su Fara Duban Jinjirin Watan Ramadan Ranar Talata

      February 16, 2026

      Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a Matsayin Sabon Shugaban NAHCON

      February 11, 2026

      Sheikh Usman Kusfa Zaria (Rigi-rigi) Ya Rasu

      February 2, 2026

      Jigawa Ta Fara Gwajin Lafiya ga Maniyyatan Hajjin 2026

      January 28, 2026
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Ba a Fasa Bututun Mai Ko Ɗaya a Niger Delta a 2025 Ba – Sojoj

      January 20, 2026

      Sojojin Najeriya Sun Ƙwato lita 290,000 Na Man Fetur a Yankin Neja Delta

      October 21, 2025

      Ƴan Bindiga Sun Ƙwace Wayoyin Ƴan Sanda a Zamfara

      October 2, 2025

      Gwamnan Kano Ya Buƙaci Tinubu Ya Tsige Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar

      October 1, 2025

      Will Using a VPN on Phone Helps Protect You from Ransomware?

      January 14, 2021
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » Ba Da Amincewar NNPP Gwamna Abba Zai Fita Daga Jam’iyya Ba – Dungurawa
    Featured

    Ba Da Amincewar NNPP Gwamna Abba Zai Fita Daga Jam’iyya Ba – Dungurawa

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanDecember 29, 2025No Comments2 Mins Read

    Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa, ya bayyana cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da duk wasu da ake zargin za su bi shi zuwa jam’iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bisa ra’ayinsu na kashin kansu. Ya ce shugabancin NNPP na jiha da ƙasa, tare da Jagoran jam’iyyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba su amince da irin wannan sauya sheƙa ba. Dungurawa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kano, ranar Litinin, da safe.

     

    Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin gwamnan da magoya bayansa sun janye wannan yunƙuri, domin mutunta jam’iyyar da kuma jama’ar Kano da suka ba su amana. A cewarsa, duk da roƙe-roƙe da nasihohi da aka yi, abubuwa sun ƙi juyawa, abin da ya sa ake ta yaɗa jita-jitar sauya sheƙar.

     

    Dungurawa ya sake roƙon gwamnan da masu shirin bin sa da su sake tunani, su “mayar da wuƙarsu kube,” su tsaya kan NNPP maimakon komawa jam’iyyar APC wadda ya ce jama’a da masu zaɓe sun yi watsi da ita. Ya yi wannan kira ne a madadin shugabanni da magoya bayan jam’iyyar baki ɗaya.

     

    Daga ƙarshe, shugaban NNPP na Kano ya karyata jita-jitar da ke alaƙanta shi da wasu jiga-jigan jam’iyyar da zargin haɗa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Jagora Sanata Kwankwaso. Ya ce shi, mataimakin gwamna, Sanusi Surajo, Sanata Rufai Hanga da sauran su ba su taɓa haɗa kowa da jagora ba, yana mai kalubalantar duk mai iƙirarin haka da ya fito da hujja.

    NNPP
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleGwamnatin Tarayya Ta Horas da Dakaru 7,000 Domin Daƙile Ta’addanci a Dazuka
    Next Article Ƴan Najeriya Za Su Ci Moriyar Rikicin Da Ake Kan Farashin Man Fetur — NNPCL
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Mutane 4 Sun Mutu a Turmutsutsun Karɓar Sadaka a Katsina

    March 2, 2026
    Featured

    Ba Za Mu Bayar da Tabbacin Sahihin Zaɓe a 2027 Ba – Amupitan

    March 2, 2026
    Featured

    Jirage Marasa Matuƙa Sun Kai Hari Matatar Man Saudiyya

    March 2, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202543 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202541 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202532 Views

    NAFDAC Ta Yi Gargaɗi Kan Wani Kororon Roba Me Matuƙar Haɗari Ga Lafiya

    December 30, 202527 Views

    An Gano Motar Ofishin Mataimakin Gwamna Da Aka Sace

    November 12, 202527 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2026 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.