Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya ce hukumar ba za ta iya tabbatar da cikakken zaɓe ɗari bisa ɗari ba a 2027 dangane da tura sakamako ta na’ura ba. Ya bayyana haka ne a taron jin ra’ayin jama’a da Civil Society Network on Election Integrity ta shirya a Abuja.
Ya ce duk da haka, zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance mafi kyau a tarihin Najeriya. Amupitan ya buƙaci a samar da doka cikin harshe mai sauki domin kowane ɗan ƙasa ya fahimci tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.
Shugaban na INEC ya ce auna nasarar zaɓe na dogara ne da fara shi a kan lokaci, zaman lafiya da kuma sarrafa sakamako yadda ya dace. Ya amince da matsalolin dabaru da aka fuskanta a baya, yana mai cewa za a tabbatar da ingantaccen tura sakamako, ko da kuwa ba a lokaci guda ba.

