Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa bai san daidai shekarunsa ba, duk da cewa ya yi hasashe bisa shekarun abokan karatunsa da ke raye, waɗanda duka suna sama da shekaru 90.
A hirarsa da aka shirya cikin jerin Toyin Falola Interviews, Obasanjo ya ce, “Ban san hakikanin shekaruna ba amma zan iya kimantawa daga waɗanda suka yi karatu tare da ni… Don haka ku yi hasashen.” Duk da wannan rashin tabbas, ya cika shekaru 88 a watan Maris.
Obasanjo ya kuma bayyana muhimmancin Presidential Library da ya kafa, inda ya ce an riga an sanya dijital kayan tarihi miliyan 3, ciki har da bayanan makaranta, wasiku da ya rubuta a kurkuku, da takardun ayyukan gona da ya gudanar yayin da yake a gidan yari. Kakaki24 ta samu labarin cewa kundin zai taimaka wajen adana tarihin baya, lura da halin yanzu, da kuma ƙarfafa tunani domin gina makoma.
Tsohon shugaban ya ƙara da cewa rashin adana bayanai yadda ya kamata shi ne babban matsalar al’umma, don haka kundin zai taimaka wajen tabbatar da cewa abubuwan da suka faru a baya ba su gushe ba.

