Gwamnatin Tarayya tare da Gwamnatin Jihar Borno sun kammala dawo da ’yan gudun hijirar Najeriya daga Kamaru, inda mutane 680 suka koma garin Banki da ke ƙaramar hukumar Bama. Wadanda suka dawo sun ƙunshi gidaje 162, kuma sun iso ne daga sansanin ’yan gudun hijira na Minawao a ranar Alhamis.
Wannan dawowa ita ce kashi na huɗu kuma na ƙarshe a shirin dawo da ’yan gudun hijirar, wanda Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira da Ƙaura (NCRM-IDP) ke jagoranta tare da haɗin gwiwar UNHCR. Shirin ya fara ne a ranar 27 ga Janairu, inda aka fara da mayar da mutane 300 zuwa Pulka a ƙaramar hukumar Gwoza.
A lokacin taron bankwana a Kamaru, gwamnan yankin Far North, Minjinyawa Bakari, ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Babagana Zulum wajen tabbatar da dawowa lafiya. Gwamnatin Borno ta amince da tallafin kuɗi da kayan more rayuwa ga iyalan da suka dawo, yayin da adadin mutanen da aka mayar gaba ɗaya ya kai 3,122 zuwa ƙananan hukumomin Bama da Gwoza.

