21 ga Nuwamba 2025
Najeriya ta sake fuskantar tashin hankali a fannin lafiya, inda Hukumar NCDC ta bayyana cewa mutane 177 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar Lassa daga watan Janairu zuwa farkon Nuwamba 2025. Rahoton mako na 44 ya nuna cewa an tabbatar da sabbin kamuwa 966 a jihohi 21 da kananan hukumomi 102, lamarin da ya daga yawan mace-mace zuwa kashi 18.3 cikin ɗari — wanda ya fi na bara.
Rahoton ya nuna cewa sabbin kamuwa sun karu daga 11 a mako na 43 zuwa 12 a mako na 44, inda aka fi samun bullar cutar a Ondo, Edo da Benue. Jihohin da suka fi fuskantar kamuwa sun hada da Ondo da kashi 36%, Bauchi 21%, Edo 17% da Taraba 13%. Nau’in wadanda cutar ta fi shafa ya kasance masu shekaru 21–30, yayin da mafi ƙarancin shekaru da aka samu ya kasance shekara 1, mafi yawa kuma 96.
NCDC ta ce babu wani sabon ma’aikacin lafiya da ya kamu a wannan mako, kuma kungiyar yaki da cutar Lassa mai kunshe da bangarori da dama na cigaba da jagorantar aikin dakile barkewar cutar a matakai daban-daban. Duk da cewa kamuwa ta ragu idan aka kwatanta da shekarar 2024, alkaluman mutuwa da ci gaba da yaduwar cutar na nuna kalubale a tsarin kare lafiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa cutar Lassa na yaduwa ne ta hanyar abinci ko kayan gida da berayen Mastomys suka gurɓata. Kasashe da dama a yammacin Afirka na fama da wannan cuta, lamarin da ke nuna bukatar karin matakan gaggawa da wayar da kai domin kare al’umma daga daya daga cikin cututtuka mafi hatsari a nahiyar.

